Gobara ta tashi a gidan gwamnan Kano mai barin gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda tai sanadiyyar asarar kadarori na miliyoyin Naira.
SOLACEBASE ta rawaito cewa gidan na kan titin Miagun, bayan Kano Club, a unguwar Nasarawa GRA, wanda ta kone wani sashi na gidan.
Gobarar dai ta tashi ne da yammacin ranar Litinin, in da ta kone kaya na miliyoyin Naira.
Majiyar mu ta shedamana cewa gobarar ta fara tashi daga wani sashi na gidan inda Ganduje yake kiwon dabbobi.
“Har yanzu bamu kai ga gano abinda ya hada gobarar ba, kawai dai ta fara ne yayin da ake aikin walda a gidan, saboda ana gyara gidan domin nan Ganduje zai dawo bayan ya miki mulki.” Inji majiyar mu
Yayin da muka tun tubi sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar a yau Alhamis, ya ce baya gari abin ya faru.
Amma yayi mana alkawarin karin bayani bayan ya yi magana da Ganduje.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na hukumar dake kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf, ya tabbatar mana da faruwar lamarin, inda yace tuni suka kashe wutar a lokacin da suka isa gidan.













































Ance sau biyu kenan cikin kwanaki 7, akwai lauje cikin naɗi, idan Abba yazo Yakamata ya bincika dalilin wannan gobarar????
Allah Ya kiyaye gaba