Abin da ya sa muka rinƙa ciyo bashi a shekaru 8 na mulkin Buhari – Zainab Shamsun

Ahmed Zainab
Ahmed Zainab

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ta kare matakin da ta ɗauka na ciwo basussuka masu ɗimbin yawa a ciki da wajen kasar a shekaru takwas da ta shafe ta na mulki.

Basussukan da aka  ta ciyo ya sanya wasu ƴan Najeriya da masana tattalin arziki sun nuna damuwa a kan matsalolin da Najeriya za ta iya fuskanta sakamakon yawan basussukan.

Sai dai  ministan kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziƙi ta ƙasa, Zainab Shamsuna Ahmed ta shaida wa BBC cewa gwamnati ta karɓo bashin ne domin hana ƙasar faɗawa cikin mawuyacin hali a lokacin da ta samu koma-bayan tattalin arziki a shekarun 2016 da 2020.

“Mun samu durƙushewar tattalin arziƙin ƙasa sau biyu, a 2016 da 2020 lokacin annobar korona, mun yi iya ƙoƙarinmu wajen ganin ƙasar ba ta faɗa cikin mawuyacin hali ba”.

“Saboda ƙasa mai girma irin Najeriya idan aka bar ta cikin wannan hali, abin zai ɓaci ne, nesa ba kusa ba”, in ji ta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here