Mukaddashin babban sufetan yan sandan Najeriya Mista Olukayode Egbetokun ya bada umarnin tura kwamishinonin yan sanda 35 zuwa jihohin kasar nan.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kakin rundunar Olumuyiwa Adejobi ya sanyawa hannu, ya kuma rabawa manema labarai ranar Talata a Abuja.
Ya ce hakan ya biyo bayan shawara da hukumar yan sanda ta bayar, kuma sufetan ya amunce. Ya kuma kara da cewa hakan zai taimaka wajan kara bada tsaro mai inganci a Najeriya.













































