Gwamnatin Borno ta tabbatar da mutuwar kwamishinan (RRR), Ibrahim Idriss-Garba, wanda ya mutu a tsakar daren Juma’a.
Malam Isa Gusau, mai magana da yawun Gwamna Babagana Zulum, wanda ya tabbatar da labarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce rundunar ‘yan sanda ta fara gudanar da bincike na gaggawa kan al’amuran da suka shafi mutuwarsa.
Gusau ya ce Zulum ya samu labarin ne cikin tsananin kaduwa da bakin ciki, inda ya kara da cewa, “Gwamnan na bakin ciki tare da iyalan marigayi kwamishinan, da sauran masoyansa, abokan arziki, abokan hulda, da mambobin majalisar zartarwa ta jihar.”