Majalisar Wakilai ta nemi gwamnantin tarayya ta dakatar da amincewa da karin kudin kiran waya

HOUSE OF REPS MEMBERS 720x430

Majalisar wakilai ta bukaci ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin na zamani ta tarayya da ta dakatar da amincewar da aka baiwa kamfanonin sadarwa (Telecom) na kara kudin kira da kashi 50 cikin dari.

Majalisar ta zartar da kudurin ne yayin zamanta na ranar Talata bayan amincewa da wani kudiri mai muhimmanci ga jama’a.

Oboku Oforji, dan majalisar wakilai na jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Yenagoa/Opokuma na jihar Bayelsa ne ya gabatar da wannan kudiri.

A watan Janairu, jukumar kula da sadarwa ta kasa (NCC) ta amince da bukatar da kamfanonin sadarwa suka yi na kara kudin kira tun bayan da aka yi nazari a kai a shekarar 2013.

Karin karatu: Majalisar Wakilan Najeriya ta bayar da shawarar ƙirƙiro sabbin jihohi 31

Bosun Tijani, ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin dijital, ya ce: “Sabon karin kudin zai baiwa kamfanonin sadarwa damar saka hannun jari a sabbin ababen more rayuwa da inganta hanyoyin sadarwa”.

Da yake gabatar da kudirin, Oforji ya ce amincewa da jadawalin karin kuɗin bai dace ba saboda masu siye suna kokawa da matsalar tattalin arziki da rashin isar da sabis na hanyar sadarwa.

Dan majalisar ya ce dole ne kamfanonin sadarwa su inganta aikinsu, kuma su magance kalubalen da ake fuskanta kafin su kara kudin kiran.

Da yake adawa da kudirin, Dominic Okafor daga jihar Anambra, ya ce karin kudin ya zama dole domin ingantacciyar hidima.

Ya ce kamata ya yi a bar kamfanonin sadarwa su kara kudin haraji, ko da yake ba a kai kashi 50 cikin dari ba.

An amince da kudirin ne lokacin da Tajudeen Abbas, kakakin majalisar ya kada kuri’a.

Daga bisani, majalisar ta bukaci ma’aikatar tattalin arziki na zamani da hukumar sadarwa ta kasa(NCC) da su dakatar da karin kudin sadarwar har sai an inganta ayyukansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here