Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai yi wa ‘yan Najeriya kunya ba, a dukkan alkawuran da ya dauka a yakin neman zabe a zabukan 2015 da 2019.
“Ban baiwa kowa kunya ba,” Buhari ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Adamu a lokacin da ya ziyarci Bauchi a ci gaba da taron yakin neman zaben shugaban kasa da na Gwamna na jam’iyyar APC.
‘’ Da ya ga dimbin jama’ar da suka tarbe shi a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa, Buhari ya ce hakan na nuni ne da nuna soyayya da aminci a gare shi daga ‘yan Najeriya.
Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya sanya wa hannu, mai taken, “Na yi wa ‘yan Najeriya hidima da gaskiya, in ji shugaba Buhari a Bauchi yayin da yake yakin neman zabensa a jam’iyyar APC.”
“Ina so in ambaci cewa a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011, na ziyarci dukkan kananan hukumomin, kuma a shekarar 2019, lokacin da nake neman tazarce a karo na biyu, na yi alkawarin cewa zan yi wa Najeriya da ‘yan Nijeriya hidima ga iyakar iyawata kuma har zuwa yanzu, ban bata wa kowa rai ba.”
Tun da farko a jawabinsa na maraba, Sarkin Bauchi ya bayyana jin dadinsa kan shugabannin siyasa a tsarin zamani na jihar da ke girmama masarautun gargajiya tare da ziyarar ban girma.
A cewar Dakta Adamu, hakan ya nuna a aikace na nuna kauna da mutunta cibiyoyin gargajiya.
Daga nan ne shugaban ya zarce zuwa filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa, a ci gaba da yakin neman zaben shugaban kasa da na gwamnonin jam’iyyar APC.












































