Tinubu ya tabbatar da zaɓar Kashim Shettima a matsayin wanda zai masa mataimaki

Bola Tinubu Daura
Bola Tinubu Daura

← Back

Thank you for your response. ✨

← Back

Thank you for your response. ✨

← Back

Thank you for your response. ✨

← Back

Thank you for your response. ✨

Dan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya zaɓi tsohon gwamnan Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a takarar shugaban ƙasa.

Tinubun ya bayyana haka ne ga ƴan jarida a garin Daura yayin wata ziyarar barka da Sallah da ya kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A kwanakin baya ne dai Tinubun ya ɗauki Ibrahim Masari a matsayin mataimaki duk da tun a lokacin ana ta ce-ce-ku-ce kan cewa na riƙo ne, kuma shi ma Masarin a yayin wata hira da BBC a kwanakin baya ya tabbatar da cewa a shirye yake ya bar kujerar idan aka samu wanda ya fi shi cancanta.

Tinubun ya bayyana cewa duk da bai tattauna wannan batu da Kashim Shettima ba amma ga shi ya bayyana wa ƴan jarida.

Haka ma jaridun Najeriya na ruwaito cewa shi da kansa Ibrahim Masari ya janye daga takarar da kansa a wata wasiƙa da ya aika wa Jam’iyyar APC a ranar Lahadi.

Kashim Shettima dai a halin yanzu shi ne Sanata mai wakiltar yankin tsakiya na Jihar Borno.

Haka kuma Shettima ya bayar da muhimmiyar gudunmawa a yaƙin neman zaɓen Tinubu a lokacin zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here