Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya bayyana Bola Tinubu a matsayin mutumin kirki kuma mai dabara, kana ya ba shi shawara.
Tinubu, wanda ke neman gaje Buhari a zaben 2023, Kwankwaso ya bukaci ya sassautawa kansa kuma ya tafi ya kula da lafiyarsa.
Kwankwaso wanda yayi magana akan dan takarar na APC da ya zabi Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ya ce yana mamakin abin da za su yi da ya wuce na Buhari a yanzu.
“Idan ka ga abokina, Bola, ka gaya masa ya bi hankali, kula da lafiyarsa sosai kuma ka tabbatar… saboda ina kaunarsa sosai, abokina ne.”
“Wannan yakin mai tsauri ne sosai, yana da bukatar kokari sosai da dai sauransu. Ina fatan zai bi a sannu domin mu ci gaba da fafutukar tabbatar da kasa daya mai karfi da wadata a Najeriya.”










































