Kar ku mayar da dimokuradiyyar mu zuwa tsarin gwamnatin masu kudi – PRP ta gargadi hukumomin zaben jihohi

IMG 20240825 WA0088

Jam’iyyar PRP ta yi Allah-wadai kan matakin da hukumomin zabe na jihohi keyi na yunkurin aiwatar da tsarin mulkin tsirarun mutane masu-hannu-da-shuni a Najeriya.

Jam’iyyar PRP na adawa da makudan kudaden da hukumomin zaben jihohi suka kakaba na biyan fam na tsayawa takara a zaben kananan hukumomi da ke tafe.

A wata sanarwa da shugaban jam’iyyar PRP na kasa Falalu Bello ya sanyawa hannu, ya soki matakin sanya makudan kudaden, “alal misali Naira Milyan 10m ga ​​mai neman tsayawa takarar ciyaman da kuma Naira Milyan 5m ga ‘yan takarar kansiloli a Kano, da kuma karin harajin N2,000,000 ga Dan takarar ciyaman da kuma N600,000 ga ‘yan takarar kansiloli a jihar Kaduna.

A cewar sanarwar, jam’iyyar na kallon wannan mataki amatsayin babbar barazana ga cigaban dumimukradiyya, sannan a matsayin wani yunkuri da gangan na hana talakawan Najeriya shiga zabe a kananan hukumomin su.

“Hakkinmu ne a matsayinmu na jamiyyar siyasa mu fito fili mu nuna rashin amincewar mu da wannan rashin adalci, mu kuma nemi nagartaccen sauyi daga shugabanin mu.” Bello

A cewar sanarwar, jam’iyyar PRP ta yi mamakin yadda hukumomin zaben wadannan jahohin suka yi watsi da ka’idar daidaito da adalci, wadda ita ce jigon gudanar da mulkin dimokradiyya.

Jam’iyyar PRP ta yi imanin cewa ‘yancin shiga cikin tsarin zaɓe wani haƙƙi ne na ɗan adam wanda bai kamata a tauye kowa hakki ba bisa la’akari da hali ko matsayin mutum .

“Ba daidai ba ne masu neman tsayawa takara su biya wadannan kudade ba bisa ka’ida ba, tabbas hakan zai haifar da halin da masu hannu da shuni ne kawai za su iya shiga harkar takarar zabe.” Inji Bello.

Shugaban jam’iyyar na kasa ya bukaci hukumimin zabe na jihohi irin su Kano da Kaduna da su sauya adadin makudan kudade ta hanyar sanya kudaden da kowanne Dan takara zai iya siyan fom din takara a saukake.

Jam’iyyar ta bukaci jihohi da su yi koyi da hukumar zabe ta kasa INEC, wadda ba ta tsawwala irin wadannan makudan kudade ga ‘yan takarkaru ba.

Jam’iyyar PRPn ta yi barazanar garzayawa kotu idan hakan ta taso, ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su shiga fafutukar kwato ‘yancin dimokradiyya, inda ta bukaci shugabanni amkwanne mataki su fifita muradun jama’a fiye da son ran su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here