Wasu ‘yan majalisar wakilai biyu sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas ne ya sanar da sauya shekar su a cikin wata wasika da aka karanta a zauren majalisar a ranar Talata.
‘Yan majalisar dai sun haɗa da Adamu Tanko mai wakiltar Suleja, Gurara, da Tafa a jihar Neja, da Jallo Husseini Mohammed, mai wakiltar mazabar Igabi ta Kaduna, sun bayyana sauya shekar tasu ne a wata wasika da kakakin majalisar Dakta Tajudeen Abbas ya karanta a zauren majalisar.
Karanta: Kana zubar da ƙimar mahaifinku a Arewa – Adnan ga Seyi Tinubu
Da suke bayyana rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar PDP a matsayin dalilinsu na sauya sheka jam’iyyar, masu sauya shekar sun kuma bayyana cewa akidunsu na siyasa a yanzu sun fi dacewa da na APC.