Yanayin siyasa a Jihar Rivers ya sake sauyawa a ranar Alhamis bayan mambobin Majalisar Dokokin Jihar suka fara daukan matakan tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Ngozi Odu bisa zargin aikata manyan laifuffuka.
A zaman majalisa da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Rivers, Martins Amaewhule, ya jagoranta, shugaban masu rinjaye Major Jack ya karanta sanarwar zarge-zarge da manyan laifuffuka da aka jingina wa gwamnan.
Majalisar ta jingina matakin da ta ɗauka da sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Nijeriya, inda Major Jack ya lissafa maki bakwai na abin da aka bayyana a matsayin manyan laifuffukan da ake zargin Gwamna Fubara da aikatawa.
Daga cikin zarge-zargen da aka ambata akwai rusa ginin majalisar dokoki, kashe kuɗaɗe ba tare da tanadin kasafin kuɗi ba, hana kuɗaɗen da suka kamata a bai wa Hukumar Hidimar Majalisar Dokoki, da kuma ƙin bin hukuncin Kotun Koli kan ’yancin kuɗin majalisar.
Zuwa yanzu rahotanni sun bayyana cewa mambobi ashirin da shida na Majalisar Dokokin Jihar Rivers ne suka sanya hannu a takardar sanarwar zargin da aka gabatar, kuma kakakin majalisar ya ce za a isar da sanarwar ga gwamnan cikin kwanaki bakwai.
Haka kuma, mataimakiyar shugaban masu rinjaye Linda Stewart ta gabatar da wata sanarwar zargin manyan laifuffuka kan mataimakiyar gwamnan, inda aka zarge ta da kashe kuɗaɗen jama’a ba bisa ka’ida ba, hana majalisa gudanar da ayyukanta na kundin tsarin mulki, da kuma haɗa baki wajen barin mutane marasa izini su mamaye ofisoshi ba tare da tantancewa daga majalisar halastacciya ba.













































