Tsohon shugaban ƙasa Jonathan da wasu shugabannin Afrika sun makale a Guinea-Bissau bayan juyin mulki

Goodluck Jonathan in Guinea Bissau 750x430

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na cikin jerin shugabannin Afrika da suka makale a ƙasar Guinea-Bissau bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Laraba.

Jonathan yana cikin tawagar mutane 36 da suka haɗa da wakilan ƙungiyar tarayyar Afrika, ƙungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika da ƙungiyar dattawan yammacin Afrika da suke sa ido kan zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar Lahadi.

Sojoji sun karɓi mulkin ne bayan shugaban ƙasa Umaro Embaló da ke neman tazarcen mulki da kuma babban abokin hamayyarsa Fernando Dias duka suka bayyana kansu a matsayin masu nasara alhali hukumar zaɓe ba ta fitar da sakamako a hukumance ba.

Wannan rikici ya sa rundunar soji ta rufe iyakoki tare da kulle filayen jiragen sama.

Wani malamin kimiyyar siyasa da yake cikin tawagar sa ido ta ƙungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika a Guinea-Bissau ya faɗa wa jaridar Solacebase a hira ta wayar tarho cewa suna tattaunawa da hukumomi domin a ba su damar barin ƙasar cikin gaggawa.

Labari mai alaƙa: Sojoji sun sanar da karɓe mulki a Guinea-Bissau

Ya ce rikicin ya faru ne jim kaɗan bayan kammala ganawar da suka yi da manyan ’yan takara biyu da suka bayyana shirin karɓar sakamakon da jama’a suka zaɓa.

Tawagar hadin guiwa ta bayyana damuwa kan abin da ya faru tare da kira ga ƙungiyar tarayyar Afrika da ƙungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika su ɗauki matakan gaggawa don dawo da tsarin mulki a ƙasar.

Haka kuma tawagar ta nemi a saki duk jami’an gwamnati da aka tsare a lokacin da juyin mulkin ya faru.

Masu sa ido na shirye-shiryen barin ƙasar Guinea-Bissau a ranar 29 ga watan Nuwamba, matuƙar hukumomin soja suka ba su izinin tafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here