Ƙungiyar ƴan asalin Masarautar Ilori da ci gabanta ta kaddamar da tara Naira miliyan 500 don aikin ci gaban Kano

WhatsApp Image 2025 10 19 at 13.46.04 750x430

Ƙungiyar ƴan Asalin Masarautar Ilori ta da ci gabanta (IEDPU) reshen Kano ta gudanar da babban taron kaddamar da tara kuɗi da nufin samar da Naira miliyan 500 domin gina babbar cibiyar ci gaban al’umma a jihar Kano.

Shugaban ƙungiyar a Kano, Sheikh Abdulwahab Abdurraheem, ya bayyana cewa an shirya taron ne domin tara kuɗin ginin da zai haɗa masallacin Jumu’a, makarantar Islamiyya, ɗakin karatu, da kuma ofishin ƙungiyar domin amfanin al’ummar Ilori da ke Kano.

Ya ce sun shafe fiye da shekaru 50 a Kano ba tare da suna da ofishi na dindindin ba, don haka suka yanke shawarar gina cikakkiyar cibiyar da za ta ƙunshi masaukin baƙi da sauran abubuwan more rayuwa.

Ya ƙara da cewa an kiyasta kuɗin aikin gaba ɗaya zai kai Naira miliyan 500.

Yayin taron, an samu halartar mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Abdussalam Gwarzo wanda ya wakilci gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf, tare da sauran baki daga sassa daban-daban.

Mai martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, wanda aka wakilta da shugaban IEDPU na babban birnin tarayya Abuja, ya jaddada muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya a cikin al’umma, tare da yabawa ƙungiyar bisa wannan yunkuri.

Shugaban jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Haruna Musa, wanda sakataren jami’ar, Malam Haruna Aliyu, ya wakilta, ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar wajen raya al’umma, yana mai cewa aikin zai amfani ba kawai al’ummar Ilori ba, har da sauran jama’ar da ke Kano.

Ya kuma sanar da cewa jami’ar za ta bayar da gudummawar Naira miliyan ɗaya ga aikin.

Haka nan, Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda Alhaji Abdulkadir Ibrahim Mahmoud ya wakilta, ya nuna farin ciki da wannan shiri tare da yi wa masu aikin addu’ar samun nasara da albarka.

Taron ya samu halartar fitattun ‘ya’yan masarautar Ilori, abokai da masoya da suka taru domin nuna goyon baya.

Haka kuma an gudanar da wasannin gargajiya da sakonnin taya murna daga shugabannin al’umma.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here