An sanar da rasuwar Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, wanda ya rasu yana da shekara 56 bayan fama da jinya a Lagos.
An haifi Lagbaja a ranar 28 ga watan Fabrairu, 1968, ya fara hidimarsa a shekarar 1987 a makarantar horas da sojoji ta NDA, kuma aka nada shi Laftanar na biyu a 1992.
Ya taka rawa a ayyukan tsaro daban-daban kamar Operation ZAKI a Benue, Lafiya Dole a Borno, da sauran su.
Lagbaja ya bar matarsa, Mariya, da ‘ya’ya biyu. Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalansa da rundunar sojoji, yana jinjina wa gudunmawarsa ga kasa.