Kamfanin rarraba wutar lantarki a Kaduna (KAEDCO), ya maido da wutar lantarki a dukkan jihohin da ke da ikon amfani da wutar lantarkin karkashin sa.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa kamfanin ya kuma yi alkawarin sake duba ayyukan da ya yi a baya.
NAN ta kuma ruwaito cewa an cimma matsayar ne bayan Gwamna Uba Sani ya kira wani taro da bangarorin biyu a ranar Juma’a.
Idan dai ba a manta ba, kungiyoyin kwadago na Kaduna sun fara yajin aikin tun ranar Lahadi.
Karanta har wa yau: Najeriya Ta Fi Kowace Ƙasa Arhar Wutar Lantarki a Duniya – Gwamnatin Tarayya
Hakan ya biyo bayan matakin da hukumar ta dauka na korar ma’aikata 444, wanda hakan ya jefa jihohin Kaduna, Zamfara, Sokoto da Kebbi cikin duhu, biyo bayan katsewar wutar lantarki.
A karshen taron, Sani ya yi alkawarin zama a tsakiya domin zai tabbatar da yin adalci ga bangarorin biyu bayan da bangarorin biyu suka amince su zauna tare da yanke shawarar hadin gwiwa.
Taron ya kuma yi nuni da cewa, dole ne a samu bayar da tallafi a bangaren gudanarwa da ma’aikata domin a samu sulhu cikin lumana a kan takaddamar.
Yarjejeniyar ta samu sa hannun Abubakar Hashidu, Manajan Daraktan Kamfanin rarraba wutar lantarki, sai Wisdom Nwachukwu, Mataimakin Shugaban kamfanin da Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) da Rilwanu Shehu, Mataimakin Shugaban Kungiyar Manyan Ma’aikatan Wutar Lantarki da Kamfanonin Sadarwa na Arewacin kasar nan(SSAEAC).
Sauran mambobin kungiyar da suka rattaba hannu kan kudirin sun hada da Muhammed Musa, mataimakin shugaban kungiyar NUEE ta Arewa da Haruna Ahmed Tinau, mataimakin babban sakataren kungiyar na Arewa, sai kuma Idris Ahmed-Idris, Manajan Daraktan Kamfanin Samar da Wutar Lantarki ta Kaduna shi ma ya sanya hannu a kan kudirin.(NAN)