A ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga Abuja zuwa Banjul na kasar Gambia, domin halartar bikin rantsar da shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, bayan sake zabensa a karo na biyu.
Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Buhari Sallau ne ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi ne da safiyar Laraba.
Haka zalika wata sanarwar da aka fitar jiya Talata a Abuja mai dauke da sa sannun Malam Garba Shehu, mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya ce: “A bisa gayyatar mai masaukin nasa, shugaba Buhari zai kasance babban bako na musamman a wajen bukukuwan da wasu shugabannin kasashen Afirka za su halarta a filin wasa na Independence, Bakau. .”
Buhari tare da wasu shugabannin kungiyar ECOWAS, sun taka rawa wajen maido da mulkin dimokuradiyya a Gambia a shekarar 2017, bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya ki mika mulki bayan ya sha kaye a zabe.
Shugaban zai samu rakiyar Ministan Harkokin Waje, Mista Geoffrey Onyeama; Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj.-Gen. Babagana Monguno; Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Amb. Ahmed Rufa’i, da sauran manyan jami’an gwamnati.
Ana sa ran shugaban zai dawo kasar a karshen bikin rantsar da shi.












































