‘Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 34 da ya yi yunkurin cinnawa wani masallaci wuta a birnin Dresden na Jamus.
A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan, mutumin a yammacin ranar Talata, 9 ga watan Mayu, 2023, ya antayar da fetur gaban wani masallaci tare da kokarin cinnawa ginin wuta.
Shaidun gani da ido sun kira lambar hukumar bayar da agajin gaggawa bayan da suka ga mutumin yana zuzzuba fetur a wajen masallacin.
An kama mutumin mai shekaru 34, kuma yana cigaba da shan bincike karkashin hukumar ‘yan sanda kan yunkurin tada kayar baya.
Duk da cewa da farko ba a san dalilinsa ba, an ce wanda ake zargin ya kona kwafin Alkur’ani mai girma a wani masallaci a watan Afrilu.













































