Hukumar kula da yanayi ta ƙasa NiMet ta yi hasashen samun yanayin rana tare da ƙura a sassan ƙasar nan daga ranar Lahadi zuwa Talata.
A cikin rahoton hasashen yanayi da hukumar ta fitar a ranar Asabar a Abuja, NiMet ta bayyana cewa yankin Arewa zai samu cikakken hasken rana a duk tsawon lokacin, yayin da ake sa ran yanayin ƙura a jihohin Arewa ta Tsakiya.
Hukumar ta kuma nuna cewa a safiyar ranar Lahadi za a samu tsawa tare da ruwan sama kaɗan a wasu sassan jihohin Ribas, Bayelsa da Delta.
Daga baya a ranar Lahadi, ana sa ran samun tsawa a wurare daban-daban na jihohin Ribas, Delta, Cross River, Akwa Ibom da Bayelsa.
A ranar Litinin, NiMet ta hasashen ci gaba da samun rana a Arewa da kuma yanayin ƙura a Arewa ta Tsakiya, yayin da jihohin Kudu za su fuskanci gajimare da safe sannan tsawa a wasu wurare daga baya a rana.
A ranar Talata, hukumar ta bayyana cewa yanayin rana da ƙura zai ci gaba a Arewa da Arewa ta Tsakiya, yayin da a Kudu za a samu gajimare da safe sannan tsawa tare da ruwan sama matsakaici daga baya.
NiMEat, ta bada shawarwarin ɗaukar matakan kariya ga masu fama da cututtukan numfashi da kuma gargadin direbobi da kamfanonin jiragen sama su bi rahotannin yanayi na NiMet.
NAN













































