Kamfanin harkokin sadarwa na FRIDABS SolaceBase Communications Limited, da ke wallafa jaridar SolaceBase a Internet, ya jaddada kudirinsa na tabbatar da aikin jarida mai da’a, kwarewa da tasiri yayin da gudanar da bitar ayyukan su a karshen shekara ranar Lahadi a Kano..
Taron bitar, wanda ya haɗa shugabanni da ma’aikata, an shirya shi ne domin tantance yadda kamfanin ya gudanar da ayyukansa a shekarar da ta gabata tare da shirye-shiryen bankwana da shekarar bisa tubalin ɗabi’a da gaskiya a aikin jarida.
Da yake magana yayin taron, shugaban kamfanin Mallam Abdullateef Abubakar Jos, ya bukaci ma’aikata su ci gaba da kiyaye gaskiya, ƙwarewa da daidaito a rahotanninsu, inda ya bayyana cewa aikin jarida mai tsari shi ne ginshiƙin da aka gina Solacebase a kansa.
Ya jaddada muhimmancin ƙara ƙoƙari wajen samar da labarai masu sahihanci, daidaito da kuma tasiri ga ci gaban al’umma, yana mai nuni da cewa amincewar jama’a ita ce mafi muhimmancin dukiyar ɗakin labarai.
Mallam Abdullateef ya yaba wa kamfanin kan labarai masu tasiri da suka kawo sauyi a al’umma, tare da ƙarfafa gwiwar ma’aikata su gina kan wannan nasara a shekara mai zuwa, sannan ya nuna godiya ga abokan hulɗa da abokan aiki bisa ci gaba da ba da goyon baya a tsawon shekarar.
A sakon sa na musamman, ya gode wa ƙungiyar bunkasa manoma ga mata ta WOFAN, tare da kamfanoni da cibiyoyi kamar UYK Holdings, El-Samad, jami’ar Bayero ta Kano, jami’ar tarayya ta Kashere a Gombe, jami’ar Skyline ta Nijeriya, jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu, farfesa Sule Ya’u Sule, shirin Kano ACReSAL, ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta Kano, da sauran abokan hulɗa da suka haɗa da hukumar ICPC, hukumar korafe-korafen jama’a da yaƙi da cin hanci ta Kano, CISLAC, Media Rights Agenda, CITAD, CAJA da CHRICED.
Yayin taron, an raba kyaututtuka ga ma’aikata a matsayin godiya a ƙarshen taron.













































