Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta sanar da korar ma’aikatanta 8 daga aiki yayin da wasu 18 ta sanya musu takunkumi bisa sabawa wasu ka’idojin hukumar.
Mai magana da yawun hukumar, Kenneth Kure ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Sanarwar wadda aka fitar a madadin Babban Kwanturolan Hukumar, Isah Jere Idris, ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan amincewar da Hukumar dake kula da hukumomin tsaro na Civil Defence da ta Kula da gidajen Yari ta Kasa da Kashe gobara da Kuma hukumar da shige da fice (wato CDCFIB) ta yi.
Inda hukumar ta CDCFIB, tace halayen ma’aikatan ya kasance mara kyau, saboda haka hukumar ba ta yarda da su a matsayin membobin ta ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Shugaban hukumar kula da shige da fice ta kasa, Isah Jere Idris MFR ya sanar da korar wasu ma’aikata takwas (8) da aka yi daga ma’aikatar tare da sanya takunkumi ga wasu 18 da aka samu da aikata laifukan da suka saba wa da’a. “
Haka kuma, an umurci wani Babban Sufuritanda na Shige da Fice da ya yi ritayar dole yayin da wasu Ma’aikata tara aka rage musu matsayi.
Ma’aikatan sun hada da Wani mataimakin Sufuritanda na hukumar wato II (ASI2) wanda aka rage masa mukami zuwa mukamin Sufeto na Shige da Fice, da wasu Sufetoci biyu da aka rage musu mukamin zuwa Mataimakan Sufeta, da kuma wasu kananan Ma’aikata shida (6) da aka umarce su da su bar matsayinsu na yanzu.













































