Ƙungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta fara yajin aikin gargadi na kwana biyar a yau, bayan ƙarewar wa’adin da ta ba gwamnatin tarayya kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da walwalar ma’aikata.
A cikin wata sanarwa mai taken “Bayyanar fara yajin aiki” da Sakatare Janar na kungiyar, Dr. Oluwasola Odunbaku, ya sanya wa hannu, NARD ta tabbatar da cewa yajin aikin ya fara ne da misalin ƙarfe 8 na safiyar Juma’a.
Kungiyar ta umarci shugabannin cibiyoyi su jagoranci mambobinsu yadda ya dace.
Daga cikin korafe-korafen akwai rashin biyan kuɗin horo na 2025, bashin watanni biyar na sabon tsarin albashin CONMESS, da kuma alawus na ƙwararru da na haɗari da ake biya musu.
Labari mai alaƙa: Yajin aiki: Likitoci sun baiwa gwamnatin tarayya sabon wa’adin awanni 24
Kungiyar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan wani taron gaggawa ta kafar intanet na majalisar zartarwa (E-NEC) da ya ɗauki sa’o’i shida, inda ta dora laifi kan gwamnatin tarayya saboda kin cika alƙawuran da aka jima ana jira.
Tun farko NARD ta ba da wa’adin kwana 21 a watan Yuli 2025, daga bisani ta ƙara masa kwana 10, wanda ya ƙare ranar 10 ga Satumba.
Ta kuma ba gwamnati ƙarin sa’o’i 24, amma hakan ya ƙare ranar Alhamis, 11 ga Satumba, ba tare da an samu wani sauyi ba.
Kungiyar ta bayyana takaici cewa duk da waɗannan tsawaita wa’adin, gwamnati ta kasa magance matsalolin walwalar likitocin, lamarin da ya tilasta musu shiga yajin aikin gargadi.














































