Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amincewa gwamnatin tarayya ta karbe ragamar gudanarwar filin jirgin saman jihar Gombe.
Gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai na gidan gwamnatin jihar bayan ganawarsa da shugaban kasar.
Yahaya ya ce matakin zai tabbatar da samar da kudaden da za a kula da ginin a duk tsawon lokacin gudanar da aikin sifiri a filin.
Idan za a iya tunawa, jami’an hukumar kula da sifirin jiragen sama ta Najeriya sun duba wasu cibiyoyi a filin jirgin saman Gombe a kwanan baya tare da ba da takardar shaidar jigilar alhazan jihar zuwa Saudiyya a watan Yuni.
Gwamnan ya kara da cewa rundunar sojojin saman Najeriya na gina sansanin sojin sama a harabar filin jirgin yayin da ake sa ran karin kayan aiki don inganta harkokin gudanarwa da kasuwanci.
Ya kuma bayyana cewa ci gaban siyasa a Gombe wani muhimmin al’amari ne da tuni suka tattauna batutuwan da shugaban kasa.
Ya kara dacewa za a gudanar da taron zuba hannayen jari na jihar Gombe a makon farko na watan Oktoba.
A cewarsa, taron zai jawo hankalin masu zuba jari, kuma a karshe za a kara yawan kudaden shiga da ake samu a jihar dake arewa maso gabas, sakamakon rikicin da aka shafe shekaru 13 ana yi a yankin.










































