Kotu ta Bayar da Belin Mawaki Ice Prince, ta kuma Saka Ranar Cigaba da Shari’a

31095e1a9f50b800
31095e1a9f50b800

Mawakin gambaran Najeriya Ice Prince, an sako shi da gidan gyaran hali na Ikoyi dake jihar Legas bayan cika sharuddan beli.

Fitaccen mawakin yana fuskantar kotun majistare dake Ajah a kan zargin aikata laifuka uku da suka hada da zargin cin zarafi, hana ‘dan sanda yin aikinsa da kuma garkuwa da mutum.

Ice Prince, wanda asalin sunansa Panshak Zamani, ‘yan sandan jihar Legas sun kama shi a ranar 2 ga watan Satumba, TVC ta rahoto.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Benjamin Hundeyin, yace a lokacin da mawakin ya ci zarafin ‘dan sandan, ya yi barazanar wurga shi cikin ruwa.

An gurfanar da shi a ranar Juma’a da ta gabata kuma kotun tun farko ta amince da bada belinsa kan kudi N500,000 sannan ya samar da tsayayyu biyu.

Kotun ta bayar da umarnin garkame shi a gidan gyaran halin Ikoyi har sai ya cika sharuddan beli.

A yayin da aka cigaba da shari’ar a ranar Laraba, lauyan masu kara sun bukaci kotu da ta dage sauraron shari’ar saboda rashin zuwan masu bada shaida biyu zaman kotun.

A yayin zaman kotun, Folarin Dalmeida, wanda shi ne lauyan mawaki, ya gabatar da tsayayyun biyu kamar yadda kotu ta bukata a matsayin sharadin belin.

Daga bisani an mayar da Ice Prince gidan gyaran hali na Ikoyi har zuwa lokacin da za tantance tsayayyn biyu.

Lauyan wanda ake karar daga bisani ya sanar da TVC cewa an saki Ice Prince daga bisani a ranar Alhamis wurin karfe 3 na yamma. An dage sauraron shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Oktoba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here