Lasisin tace Mai aka bai wa Dangote ba na Sifurinsa ba- Dallalan Mai

Dangote refinery CNG truck 750x430

Dillalan man fetur a karkashin kungiyar Masu depo-depo na man Fetur ta Najeriya PETROAN sun bukaci Gwamnatin Tarayya da masu kula da masana’antu da suka hada da Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya NMDPRA da su dakile yunkurin da matatar man Dangote ke yi na yin dakon man fetur da dizal kyauta ga gidajen sayar da mai da kuma masu yin amfani da shi a fadin kasa.

Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya ce “Idan kamfani daya mai girma kamar na dan uwanmu Aliko Dangote zai iya yin duk wannan, to tabbas zai kore mu daga wannan kasuwanci,” in ji Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harry, a cikin shirin Brief na gidan talabijin na Channels a yau Talata.

Ya ce, matakin da matatar dangote ta dauka na fara dakon man fetur kyauta nan da watan Agusta zai haifar da asarar guraben ayyukan yi da kuma zama.

A ranar Lahadi, 15 ga Yunin bana ne matatar man wadda ke a birnin Lagos ta sanar da kai man fetur da dizal kyauta ga ‘yan kasuwa da dillalai da sauran manyan masu amfani da shi a fadin kasa.

Matatar man, wadda ke tace adadin ganga 650,000 a kowace rana ta ce. ta sayo sabbin tankunan dakon mai masu amfani da iskar gas ta CNG don fara shirin a ranar 15 ga Agustan bana.

Har ila yau, ta ba da damar rance ga waɗanda ke siyan mafi ƙarancin lita 500,000 wajen ba su damar samun ƙarin lita 500,000 a kan bashi na tsawon makonni biyu, ƙarƙashin amincewar bankuna.

Tuni dai ‘yan kasuwar man fetur da masu manyan motoci suka yi kakkausar suka ga yunkurin fadada matatar man dangote, inda suka ce za ta kashe masu gidajen man, da manyan motocin dakon kaya, da masu sana’ar sayar da man fetur da dizal kai tsaye ga manyan kamfanoni da sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here