Dalilan dasuka sanya Tinubu fita kasar waje – Mataimaki na musamman

Tinubu 750x430 2
Tinubu 750x430 2

Zababben shugaban kasa, Sen. Bola Tinubu, ya bar Najeriya domin zuwa aikin umara a kasar Saudiyya, tare da gudanar da shirin mika mulki, gabanin kaddamar da ranar 29 ga watan Mayu.

Mista Tunde Rahman, mai taimaka masa kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja, inda ya kara da cewa zababben shugaban ya bar filin jirgin sama na Murtala Mohammed ya nufi Turai.

“Zababben shugaban kasar ya yanke shawarar yin hutu ne bayan yakin neman zabe da lokacin zabe domin ya huta a Paris da Landan.

“Shirye-shiryen zuwa Saudi Arabiya don Umrah da kuma Azumin Ramadan da zai fara ranar Alhamis.

“Yayin da zai tafi, zababben shugaban kuma zai yi amfani da damar wajen tsara shirin mika mulki,” in ji Rahman.

Ya gargadi kungiyoyin yada labarai da su guji yada jita-jita, labaran karya da ikirari marasa tushe, inda ya bukace su da su rika neman karin haske daga ofishin yada labarai na Tinubu kafin su buga.

Rahman ya ce zababben shugaban kasar ya umurci dukkan manyan mataimakansa da ma’aikatan yakin neman zaben da su je dan huta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here