Alex Otti na jam’iyyar Labour Party (LP) ya lashe zaben gwamnan jihar Abia da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.
Rahotanni sun nuna yadda Otti ya doke abokan hamayyarsa kamar Okey Ahiwe na jam’iyyar PDP da Enyinnaya Nwafor na jam’iyyar matasa (YPP).
Otti ya samu kuri’u 175,467, Ahiwe ya samu kuri’u 88,529 yayin da Nwafor ya samu 28,972.
Jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a jihar, Farfesa Nnenna Nnannaya-Oti ta bayyana Otti a matsayin wanda ya lashe zaben da yammacin ranar Laraba a yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a Umuahia, babban birnin jihar Abia sama da sa’o’i 48 bayan kammala tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Abia.
Wanda shine karo na biyu da LP tayi gwamna a cikin shekaru 20 da suka gabata wanda Olusegun Mimiko ya zama gwamnan jihar Ondo daga watan Fabrairun 2009 zuwa Fabrairu 2017.
A halin yanzu dai an bayyana sakamakon zaben gwamnoni 25 cikin 28 da aka gudanar. APC ta samu nasara a jihohi 15, PDP a takwas, LP a daya yayin da New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta lashe Kano.













































