Dalilan da ya sa Naja’atu Muhammad ta fice daga APC

Najatu Mohammed
Najatu Mohammed

Naja’atu Mohammed ta mika takaddar ajiye aiki tareda ficewa daga jam’iyyar APC tare da bayyana ficewar ta daga harkokin siyasa.

Uwargida Mohammed ta kuma yi murabus daga yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu inda ta kasance daraktar hulda da jama’a.

Sanarwar murabus din ta na zuwa ne a wata wasika da ta aikewa shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu.

Ta yi nuni da cewa abubuwan da suka faru a fagen siyasar kasar a baya-bayan nan ya sanya bazata iya cifaba da shiga harkokin siyasar bangaranci ba.

“A bisa ka’ida dakuma sashi na 9.5 (i) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC, na rubuto muku ne domin in sanar da ku ficewa ta daga jam’iyyar APC.

“Ina kuma amfani da wannan wasiƙar kuma na sanar da ku murabus na a matsayin Darakta na Hukumar Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa ta APC.

Cikin sanarwar Naja ta kuma ce ta fice daga siyasar jam’iyyar ne saboda manyan jam’iyyun ba su da wa ta akida da ta bambanta su da juna.

“Jam’iyyun siyasarmu ba su da bambance-bambancen akida kuma kawai riguna ne da ‘yan siyasa ke sanyawa don biyan bukatunsu a kowanne lokaci. A dalilin haka ne muke ganin ‘yan siyasa suna canjawa daga wannan riga zuwa waccan a duk lokacin da suke so. In ji ta

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here