Kar ku Amince PDP ta dawo mulki – Tinubu ga Alummar Jigawa

Bola Tinubu new new
Bola Tinubu new new

Dan takarar shugaban kasa a jamiyyar APC Asiwaju Bola Tinubu ya bukaci al’ummar jihar Jigawa da su kada kuri’unsu wajen zaben shugabanni masu gaskiya da rikon amana a zaben 2023 mai zuwa.

Jami’in yada labarai na Tinubu Mista Tunde Rahman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja, inda ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ne ya bayar da wannan umurnin a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a wani gangamin yakin neman zabe a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar da kada su bari jam’iyyar PDP ta dawo mulki.

Da yake magana game da tsare-tsaren gwamnatinsa, Tinubu ya yi alkawarin gyara harkar noma, tare da ba da kulawa sosai wajen bunkasa ababen more rayuwa a fadin kasar nan.

Ya ce za a fara aikin noma mai fadin gaske a jihar Jigawa domin ganin jihar ta zama wurin da za a yi la’akari da shi a masana’antar noma da hada-hadar aikin noma.

Ya kuma yi alkawarin cewa idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta ci gaba da samun nasarorin da aka samu a fannin noma a jihar.

Da yake jawabi, Gwamna Badaru Abubakar na Jigawa, ya godewa al’ummar jihar bisa yadda suka fito kwai da kwarkwata domin tarbar Tinubu da shugabannin jam’iyyar APC.

Ya bayyana Tinubu a matsayin uba me daraja wanda nan ba da dadewa ba zai zama “uban kasa.” ya kara da cewa zai yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here