Gwamnatin Kano ta tabbatar da bullar cutar dake sarkafe numfashi ta diphtheria a kananan hukumomi 13 na jihar.
Wannan na zuwa ne sa’o’i 48 bayan rahoton da jaridar solacebase ta bayar a ranar Alhamis, inda ya bayyana bullar cutar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 25 kamar yadda ya faru a ranar Juma’ar da ta gabata.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Tsanyawa ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa kan bullar cutar zazzabin Diphtheria da Lassa a jihar
Ya ce an samu mutane 100 da ake zargin sun kamu da cutar inda uku suka mutu.
“Ya zuwa ranar 20 ga watan Janairun 2023 mun sami rahoton bullar cutar guda 100 da ake zargi daga kananan hukumomi 13.
Kananan hukumomin sun hadar da ”Ungogo, Nassarawa, Bichi, Dala, Dawakin Tofa, Dawakin Kudu, Fagge, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Kiru, Rano, and Gwarzo.
Tsanyawa ya ce a halin yanzu majiyyata 27 suna karbar magani yayin da 41 kuma aka sallame su.
Kwamishinan ya kara da cewa, a ranar 10 ga watan Janairu, cibiyar bayar da agajin gaggawa ta kiwon lafiyar jama’a ta samu rahoton da ake zargin mutanen sun kamu da cutar zazzabin Lassa a asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase da ke Kano.
Ya ce an tura wata tawaga domin gudanar da bincike, an dauki samfurin gwajin a dakin gwaje-gwaje sannan bayan kwana uku sakamakon ya nuna sun kamu da zazzabin Lassa.
“An dauki samfura 10 daga cikin mutanen da ke da hatsarin kamuwa da cutar, 3 sun kamu da cutar, wanda adadin ya kai 4 wadanda a halin yanzu ake kulawa da su a asibitin koyarwa na Aminu Kano,” in ji Tsanyawa.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da cibiyar killace masu cutar ta Kwanar Dawaki domin killace masu cutar zazzabin Lassa.
Ya kara da cewa an horar da ma’aikatan lafiya tare da tura su cibiyar keɓewa inda kuma yayi nuni da cewa jihar za ta gudanar da aikin rigakafi na yau da kullun ga kananan hukumomin da abin ya shafa.














































