PDP ta dage zaben Shugabanninta shiyyar Arewa maso Yamma

E185853A C007 443C 8EF8 A273A0E89118
E185853A C007 443C 8EF8 A273A0E89118

Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP ya dage zaben shugabancin jam’iyyar  shiyyar Arewa-maso-Yamma da aka shirya tun farko a ranar Asabar, 12 ga Fabrairu, 2022.

Solacebase ta ba da rahoton cewa tun da farko an shirya zaben ne a ranar 20 ga Nuwamba, 2021 kafin a dage ta.

Wata sanarwa da sakataren jam’iyyar  na kasa, Hon. Umar M. Bature, ya tabbatar da dage zaben.

Sanarwar ta ce nan gaba kadan za a sanar da sabuwar ranar.

Sanarwar ta bukaci INEC da duk masu neman takara, wakilai da masu ruwa da tsaki su lura da hakan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here