Har yanzu Gbajabiamila shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa – fadar shugaban ƙasa

Femi Gbajabiamila (1)

Fadar shugaban ƙasa ta musanta rahotannin da ke yawo cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sauya shugaban ma’aikatan fadarsa, Femi Gbajabiamila, da babban sakatarensa na musamman, Hakeem Muri-Okunola.

Fadar shugaban ƙasar ta bayyana rahoton a matsayin ƙirƙirarren labari da aka yaɗa a kafafen sada zumunta domin haddasa rikici da rashin jituwa a cikin gwamnati da kuma ruɗar da jama’a.

Bayani kan hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, wanda ya bayyana cewa babu wani sauyi a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, inda Femi Gbajabiamila ke ci gaba da rike mukaminsa kamar yadda aka saba.

Haka kuma, fadar shugaban ƙasar ta jaddada cewa Hakeem Muri-Okunola shi ma yana nan a matsayinsa na babban sakataren shugaban ƙasa na musamman, ba tare da wani sauyi ko nadin sabon mutum ba.

Fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa irin wadannan rahotanni aikin masu yaɗa labaran ƙarya ne da ke da niyyar raba kan gwamnati da ɓata sunan hukumomi, tare da jawo ruɗani ga al’umma.

Ta yi kira ga kafafen watsa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta da su rika tantance gaskiyar labarai kafin wallafawa ko yaɗawa, tare da shawarartar ‘yan ƙasa su dogara da hanyoyin hukuma domin samun sahihin bayani kan harkokin gwamnati.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here