Gwamnatin tarayya zata taimakawa iyalen sojojin da suka mutu da wandan suka raunata sakamakon yaki da yan ta’adda.
Ministar harkokin jin kai da yaki da fatara Dr Betta Edu ce ta bayyana haka yayin wata ganawa da babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Christopher Musa a ranar Litinin a Abuja.
Edu ta bayyana cewa akwai bukatar a sa iyalan sojojin a cikin tsarin magance fatara da talauci da gwamnatin tarayya ta fitu dashi.












































