Gwamna Ganduje ya gabatar da kasafin kuɗin Naira Milyan Dubu 196 na shekarar 2022

ganduje presents 2021 suplementary budget to state assembly 347
ganduje presents 2021 suplementary budget to state assembly 347

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya gabatar da daftarin kasafin kudi na shekarar baɗi wato 2022 da ya kai kimanin Naira Milyan Dubu 196 gaban zauren majalisar Dokokin jihar.

Jaridar solacebase ta lura cewa kasafin kudin shekarar badin ya gaza cimma kasafin kudin shekarar bara da kusan kaso 60.

Taken kasafin na bana ‘ inganta walwala da hadin kai dan samun cigaba’ Gwamna Ganduje yace cikin daftarin kasafin kudin, za ayi amfani da Naira Milyan Dubu 107 kimanin kaso 55 domin aiwatar da manyan ayyuka yayin da sauran kaso 45 zasu tafi gurin ayyukan yau da kullum.

Gwamna Ganduje yace manyan bangarori dasuka lashe manyan kaso akasafin sun hadar da bangaren ilimi,lafiya, da ayyuka yau da kullum Inda za a kashe naira Milyan Dubu 51 bangaren ilimi wanda cikin adadin za a kashe naira Milyan Dubu 3400 wajan ciyar da daliban makarantun kwana yayin da za ayi amfani da Naira Milyan Dubu 2200 wajan aiwatar da ayyuka amanyan makarantu.

Gwamna Ganduje yakara dacewa, an ware kusan kimanin Naira Milyan Dubu 34 domin gina gadar karkashin kasa da gadar sama dakuma gina sabbin tituna inda har ma yake cewa ” Babu shakka wannan kasafin yazo akan gaba, domin kuwa kasafin zaiyi duba bangaren ilimi musamman ilimin yaya mata, lafiya, samar da abinci da tabbatar da tsaro”

Da ya waiwaya batun haraji, Gwamna Ganduje yace ” A jumlace mu na sa ran zamu tattara kudin shiga acikin wannan kasafi dasuka kai naira Milyan Dubu 146,844,501,343 wanda ya kunshi naira Milyan Dubu 33,862,079,343 amatsayin kudin haraji dazamu tattara yayin da naira Milyan Dubu 68,299,480,000 muke sa ran karba daga asusun hadaka na tarayya”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here