Mambobi 8 daga cikin 24 na majalisar dokokin jihar Plateau, sun tsige shugaban majalisar Abok Ayuba, da safiyar yau Alhamis.
Yayin zaman da ba a saba ganin irinsa ba da ya gudana da safiyar yau, karkashin mataimakin shugaban majalisar Saleh Yipmong, an zabi Yakubu Sanda (APC- Pengana) a matsayin sabon shugaban majalisar.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa, mambobin 8 sun shiga majalisar ne da misalin karfe 6 na safiya don aiwatar da shirin na su, wanda ya gudana bisa gadin jami’an tsaro.
Tun a jiya da dare, mambobin 8 suka yi yunkurin tsige shugaban, sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba, don haka, suka koma majalisar yau da safe.
A cewar Nanbol Daniel (PDP-Langtang North Central), ba zai yuwu a tsige shugaban ba,m, domin ba a bi ka’idojin da majalisar ta gindaya ba.
Har ila yau, NAN ta ruwaito cewa, akwai wani korafi dake wadari a kafafen sada zumunta da safiyar jiya, wanda wata kungiyar matasa ta Youths Rights Against Corruption (YRAC) ta gabatar, dake zargin shugaban majalisar da cin hanci da rashawa.
Kungiyar ta ce ta mika korafi ga hukumar EFCC, inda take zargin shugaban majalisar da laifukan da suka hada da amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba da kuma almundahana.
Bugu da kari, kungiyar ta bukaci shugaban majalisar ya sauka daga mukaminsa, har sai an kammala bincike.
Daraktan Zartawa na kungiyar YRAC, Abednego Musa ne ya rattaba hannu kan takardar korafin dake zargin shugaban da aikata wadancan laifuka.
Zuwa yanzu, shugaban da majalisar kanta, ba su ce uffan dangane da lamarin ba.
A daya bangaren kuma, mambobin majalisar 8, sun ce za su gabatar da sabon shugaban wato Yakubu Sanda, ga Gwamnan jihar Simon Lalong, da safiyar yau. (NAN)













































