Shugaban kasa Muhammadu Buhari l, ya ci gaba da zoyararsa a Kasar Saudiyya, inda da yammacin jiya ya tsaya a Birnin Madina, ya yi sallah, tare da addu’o’in neman dawowar zaman lafiya da tsaro a Nijeriya.
Rahoton Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa, shugaba Buhari ya sauka ne a filin jirgin saman Prince Muhammad Abdulaziz, inda ya samu tarba daga mataimakin gwaman yankin, wato Yerima Sa’ud Al-Faisal.
Rahoton ya ce shugaban wanda ke tare da tawagarsa, ya shafe lokaci mai tsawo a masallacin Manzo (SAW), yana karatun Qur’ani tare da addu’o’i.
Shugaban tare da tawagarsa, sun yi wa kasa da al’ummarta addu’a, da kuma neman dawowar zaman lafiya da tsaro a Nijeriya da duniya baki daya.
Ya kuma yi addu’ar ganin farfadowar tattalin arzikin da annoba ta taggayara, domin moriyar kasar da al’ummarta.
Ana sa ran zuwa anjima da yamma, shugaban zai isa Makkah domin gudan ar da Umrah.













































