Yunkurin yin sulhu a rikicin Sudan ya sake gazawa

1931662734949755594
1931662734949755594

Sabon yunkurin da aka yi na tabbatar da tsagaita wuta tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun Rapid Support Forces RSF ya gaza, lamarin da ya sa cikin mazauna Khartoum ya duri ruwa sakamakon rashin abinci da magunguna a birnin.

Yarjejeniyar tsagaita wutar ta awa 24 — wadda kasashe da dama da ke son kwashe ‘ya’yansu suka roki a kulla baya an kwashe kwanaki ana rikicin — ta gaza yin aiki ranar Laraba da karfe 6 na yamma a agogon kasar, duk da alkawarin da bangarorin biyu suka yi.

Ganau sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an cigaba da yin gumurzu har safiyar Alhamis.

Ma’aikatar Lafiyar Sudan ta ce an kashe kusan mutum 300 yayin da aka jikkata 2,600.

Rundunar sojin Sudan ta ce an kwashe sojojin saman Masar 177 zuwa kasarsu, kwanaki kadan bayan dakarun RSF sun sauke su a garin Merowe da ke arewacin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here