Kwamitin da’a na Majalisar Dattawa ya ba da shawarar a dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan sakamakon zargin cin zarafi da ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.
Kwamitin ya kuma ba da shawarar cewa dole ne Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta nemi afuwar majalisar dattawa saboda rashin mutunta majalisar.
A tsawon wa’adin dakatarwar, kwamitin ya bayyana cewa za’a cire mata albashi da bayanan tsaro.
Ana ci gaba da muhawara kan rahoton.
Cikakkun bayanai nanan tafe……