Gwamnan Kano ya amince da biyan Naira Biliyan 15.6 ga tsofaffin kansilolin APC sama da 3,000

WhatsApp Image 2025 04 25 at 08.51.59 750x430

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da fitar da kudi sama da Naira biliyan 15.6 domin biyan kudaden sallama da alawus-alawus na wurin kwana, da alawus-alawus na hutu ga tsofaffin kansiloli sama da 3,000 daga kananan hukumomi 44.

Za a biya kudin ga kansilolin da suka yi aiki daga a zamanin mulki guda uku: 2014-2017, 2018-2020, da 2021-2024.

Za a fitar da kudaden ne kashi uku a cikin Afrilu, Mayu, da Yunin 2025.

SolaceBase ta ruwaito cewa wadannan tsaffin kansilolin sun yi aiki ne a karkashin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, inda a lokacin ba a biya su hakkokinsu ba.

A cewar wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ibrahim Adam ya fitar a ranar Laraba, ya ce batun wadannan makudan kudade ya haifar da takaici a tsakanin ‘yan majalisar da abin ya shafa.

Karin karatu: Gwamnatin Kano ta amince da biyan alawus na tsawon watanni 11 ga masu gadin gandun daji

Gwamna Yusuf, wanda aka zaba a wani tsarin siyasa na daban, ya dauki matakin ne don daidaita abubuwan dabya riska wanda ke nuna ficewa daga tsarin mulki na baya.

Hakan ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen magance matsalolin da tsofaffin kansilolin ke fuskanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here