Majalisar dokokin jihar Rivers karkashin jagorancin kakakinta, Martin Amaewhule, ta rubutawa gwamna Simi Fubara wasika, inda ta bukaci a kori dukkan kwamishinonin jihar cikin sa’o’i 48.
Hakan na cikin wata wasika, kuma kudurin ya zo ne bayan zaman majalisar a ranar Laraba.
Majalisar ta kuma bukaci a kori wasu mukamai da ‘yan majalisar ba su tantance su yadda ya kamata ba.
Karin karatu: Yanzu-yanzu: Majalisar dokokin jihar Rivers ta ba da wa’adin awanni 48 ga Fubara don ya gabatar da kasafin kudin 2025
Don haka ne majalisar da Amaewhule ke jagoranta ta umurci Gwamna Fubara da ya gabatar da sabon jerin sunayen wadanda za a nada domin nada su a matsayin kwamishinoni cikin sa’o’i 48.
Tun da farko dai majalisar ta baiwa Fubara wa’adin sake gabatar da kasafin kudin jihar Rivers na shekarar 2025.