Majalisar dattawa ta yi watsi da karar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jam’iyyar PDP daga jihar Kogi ta Tsakiya)l ta shigar a kan shugaban majalisar dattijai Godswill Akpabio, inda ta yi zargin cin zarafinta.
Da yake magana a wani zama na bincike a ranar Laraba, Sanata Neda Imasuen na jam’iyyar LP daga jiha Edo ta Kudu kuma Shugaban kwamitin majalisar Dattawa kan Da’a da ladabtarwa da Korafe-korafen Jama’a, ya bayyana karar a matsayin wadda tazo a kurarren lokaci saboda saba doka ta 40 na Dokokin Majalisar Dattawa.
A cewar Imasuen, Akpoti-Uduaghan ta sanya hannu kan takardar da kanta a maimakon wani ya amince da ita, inda ta mayar da ita a matsayin mara inganci.
Bugu da kari ya kuma ce, batutuwan da aka gabatar a cikin koken sun rigaya sun gurfana a gaban kotu, wanda hakan ya sa aka yanke musu hukunci.
Labari mai alaƙa: Zargin lalata: Akpabio ya musanta zargin da ake masa yayin da Sanata Natasha ta shigar da kara
Duk da zaman da kwamitin ya shirya, Akpoti-Uduaghan ta kasa bayyana a gaban kwamitin binciken, wanda aka shirya farawa da misalin karfe 2:00 na rana wanda hakan ya sa ba a fara ba sai karfe 2:58 na rana lokacin da shugaban kwamitin ya iso bayan ya jira Akpoti-Uduaghan da Sanata Yemi Adaramodu, amma Akpoti-Uduaghan bata halarci zaman ba.
Tuni dai aka mika lamarin ga kwamitin da’a makonni biyu da suka gabata biyo bayan abin da Akpoti-Uduaghan ta yi a yayin zaman da aka yi. Daga nan ne shugaban majalisar dattawa Akpabio ya umurci kwamitin da ya gudanar da cikakken bincike tare da bayar da rahoto cikin makonni biyu.
A yayin tattaunawa, Adaramodu ya sanar da majalisar dattawa cewa kalubalen da Akpoti-Uduaghan ta yi wa shugaban majalisar dattawan a bainar jama’a kan sauyin kujerar da ta ke kai ya lalata martabar majalisar.
Ya kuma yi tsokaci kan wata hira da ta yi wa Brekete Family a gidan rediyo da talbijin na kare hakkin bil’adama, inda ta sake jaddada zarginta kan Akpabio.
Bayan wannan tattaunawa, majalisar ta yanke shawarar tura batun gaban kwamitin da’a, ladabtarwa, da kuma kararrakin jama’a, karkashin jagorancin Sanata Neda Imasuen, domin ci gaba da nazari.