Zargin lalata: Akpabio ya musanta zargin da ake masa yayin da Sanata Natasha ta shigar da kara

Akpabio and Natasha

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godswill Akpabio ya musanta zargin da ɗaya daga cikin sanatoci mata ta ƙasar, Natasha Akpoti ta yi kan cewa ya taɓa yunƙurin cin zarafinta ta hanyar lalata.

Akpabio ya bayyana hakan ne a farkon zaman majalisar na yau Laraba.

Akpabio ya ce “ina son shaida wa duniya cewa ban taɓa cin zarafin Sanata Natasha ko wata mace ba, mahaifiyata ta yi min tarbiyya mai kyau, saboda haka ina girmama mata”.

Kalaman shugaban Majalisar Dattaijan na zuwa ne bayan Sanata Natasha Akpoti ta gabatar da ƙorafinta ga majalisar game da zargin yunƙurin cin zarafi da take yi wa Akpabio.

Karanta: Rikicin Natasha da Akpabio: Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa ACF ta bukaci ayi cikakken bincike na gaskiya

Batun dai ya janyo muhawara mai zafi a faɗin Najeriya, tun bayan da Sanatar ta bayyana a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Arise, cewa Akpabio ya faɗa mata wasu kalamai da ba su dace ba.

Ƙungiyoyi da dama ne suka buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, yayin da wasu kuma ke ganin cewa bai kamata a ci gaba da tattaunawa kan lamarin ba.

A zaman majalisar na yau Laraba an tafka muhawara inda wasu sanatocin suka mike suka bayyana cewa bai kamata a saurari ƙorafin Natasha ba kasancewar ta shigar da ƙara a gaban kotu.

Sai dai Natasha ta kare matakin nata, inda ta ce ƙarar da ta shigar a kotu ta shafi batun ɓata suna ne da wani hadimin Sanata Akpabio ya yi, yayin da ƙorafinta ga majalisar kuma ya shafi batun yunƙurin cin zarafin lalata ne da take zargin shugaban majalisar da aikatawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here