Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda biyu don cike guraben da ake da su a ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Eno Olotu, daraktar yada labarai da hulda da jama’a, ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ce (HCSF) ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Laraba.
Sabbin jami’an da aka nada sun hada da Adeladan Olarinre da Mukhtar Muhammed.
Karanta: Tinubu ne yaƙi amincewa da naɗi na a matsayin minista, ba majalisar dattawa ba – El-Rufai
Olotu ta ce nadin ya biyo bayan zabar wanda ya yi daidai da jajircewar gwamnatin da cancanta har ma da kwarewa a aikin gwamnati.
Ta kara da cewa nade-naden da aka yi na nuna himmar da gwamnatin ta yi na samar da ingantacciyar gwamnati mai dogaro da kai wanda ya dace da bukatun ‘yan Najeriya. (NAN)