‘Yar Najeriya takafa tarhin zama wadda ta fi dadewa tana girki a duniya

0

Kundin adana muhimman abubuwan tarihi na duniya Guinness World Records ta tabbatar da ‘yar Najeriya, Hilda Bassey a matsayin wadda ta kafa tarihi wajen shafe tsawon lokaci tana girki.

Masu kula da kundin a cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Talata, sun ce “Bayan cikakken nazari kan dukkan shaidu, a halin yanzu kundin tarihin Guinness na iya tabbatar da cewa Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta karya tarihin shafe tsawon lokaci inda ta yi sa’a 93 da minti 11 tana girk.”

Hilda mai shekara 27 ta fara girkin ne a ranar Alhamis 11 ga watan Mayun 2023 kuma ta ci gaba har zuwa ranar Litinin 15 ga watan Mayu.

Ta girka abinci iri daban-daban har fiye da 100 a tsawon kwana hudu.

Hilda dai ta yi yunƙurin kafa tarihin shafe tsawon sa’a 100 tana girki ne ba tare da katsewa ba, amma sai masu kula da kundin tarihin suka cire kusan sa’a bakwai a lissafin da ta yi saboda kuskuren ƙidaya a lokacin gajeren hutu da ta riƙa yi.

Hilda ta karya tarihin Lata Tondon ‘yar Indiya wadda ta yi sa’a 87 da minti 45 tana dafa abinci ba tare da katsewa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here