CBN ya yi alkawarin samar da sababbi kuma wadatattun takardun Naira

News naira notes 750x430
  1. Babban Bankin ƙasa (CBN) ya sake jaddada aniyarsa na tabbatar da wadatar takardun Naira sabbin tare da ingantaccen tsari.

Bankin ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su zama jakadu wajen kare darajar kudin kasar.

Misis Hakama Ali, Mukaddashiyar Darakta ta sashen hulda da jama’a na CBN, ce ta bayyana haka a ranar Alhamis a wurin bikin “Rana ta musamman ta CBN” da aka gudanar a ci gaba da baje kolin kasa da kasa na kasuwanci karo na 20 a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa baje kolin ya fara ne a ranar 25 ga Satumba, kuma zai kare a ranar 6 ga Oktoba.

Ta ce CBN zai ci gaba da kokarin samar da takardun Naira sabbi, tare da kira ga ‘yan Najeriya da su mutunta kudin kasar, ba tare da yayyagasu, gurbatawa ko kuma yin jabu da shi ba.

Ta kara da cewa darajar Naira tana wakiltar alamar kasa, don haka wajibi ne a kiyaye shi a matsayin abin alfahari.

Ta ce kokarin CBN yana maida hankali ne wajen tabbatar da dorewar tattalin arziki ta hanyar karfi a tsarin kudi, daidaitaccen kasuwar musayar kudade da kuma hadin kai tsakanin hukumomin kudi da na haraji.

Labari mai alaƙa: CBN ya fara gangamin yaƙi da wulaƙanta takardun Naira da kuma ɓoye su

Ta bayyana cewa a ranar 11 ga Satumba, ajiyar kudaden waje na kasar ya karu zuwa dala biliyan 43.05, daga dala biliyan 40.51 a karshen watan Yuli 2025.

Hakazalika, ta ce CBN ya na ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da karfin tsarin bankuna a Najeriya, tare da tabbatar da cewa yawancin alamomin karfin kudi suna cikin ma’aunin da aka kayyade.

Ta ce bankuna 14 sun riga sun cika sharuddan karin jarin da aka wajabta, kuma sauran bankuna na karkashin kulawa don tabbatar da kammala aikin cikin nasara.

A nasa jawabin, Darakta-Janar na Abuja cibiyar kasuwanci da masana’antu (ACCI), Mista Agaidu Jideani, ya bayyana CBN a matsayin babban abin dogaro ga ci gaban kasuwanci.

Ya ce ta hanyar samar da rancen kasuwanci, kula da musayar kudi, da kuma dabarun hada kan al’umma, CBN na ba da dama ga kananan masana’antu (MSMEs) da sauran ‘yan kasuwa.

A cewarsa,  bankin na taka muhimmiyar rawa wajen daidaita hauhawar farashin kayayyaki da tabbatar da kwarin gwiwa a tsarin kudi, wanda ke taimakawa wajen dorewar kasuwanci a kasa.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here