Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a ranar Alhamis, ya bar Abuja zuwa birnin Addis Ababa na kasar Habasha, bisa goron gayyata a hukumance da firaministan tarayyar kasar Habasha, Dr Abiy Ali.
Sanarwar da mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Stanley Nkwocha, ya fitar ta ce, a yayin ziyarar, Shettima zai halarci bikin kaddamar da wani shiri na Green Legacy na Habasha, wani shiri na kare muhalli.
Ya yi bayanin cewa an tsara shirin ne domin yakar sare dazuka, da inganta bambancin halittu, da kuma dakile illolin sauyin yanayi, da nufin dasa bishiyoyi biliyan 20 cikin shekaru hudu.












































