Sabuwar Shekarar Musulunci: Garo ya taya Musulmi murna, ya yi kira da hadin kai da kaunar juna

Murtala Garo
Murtala Garo

Tsohon dan takarar mataimakin gwamna a shekarar 2023, Alhaji Murtala Sule Garo, ya taya daukakin al’umar Musulmi murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1447.

Garo ya bayyana hakane a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Juma’a.

“Ina taya daukacin al’ummar Musulmi murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci mai albarka, 1 ga Muharram 1447 bayan Hijira,” in ji Garo.

Ya kuma kara da cewa, “Wannan rana ce mai matukar muhimmanci duniyar Musulunci, wadda ke tunatar da mu darussan hijirar Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, wajen imani, jajircewa, da sadaukarwa.

“Ina kira da tunatarwa ga al’ummar Musulmi da mu yi amfani da wannan lokaci wajen ƙarfafa kaunar juna, tausayi da jinkai a tsakaninmu.

“Dukkan mu akwai rawar da za mu iya takawa don gina al’umma da tabbatar da zaman lafiya kamar yadda addinn Musulunci ya koyar.”

Ya kuma yi addu’ar neman zaman a jihar Kano da ma kasa baki daya.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here