Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa ya bayar da umarnin kashe shugaban kungiyar al Qaeda Ayman Zawahiri – harin da aka kai da jirgi maras matuki a Kabul, babban birnin Afghanistan ranar Asabar.
Mista Biden ya ce Ayman Zawahiri ne babban mataimakin Osama bin Laden kuma yana da hannu a harin 11 ga watan Satumbar 2001 wanda ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da dubu uku.
Shugaban na Amurka ya bayyana kashe al Zawahiri a matsayin abin da zai kwantar da hankulan iyalan wadanda suka halaka a hare-haren da al Qaeda ta kai.
Mista Biden ya kuma ce Amurka za ta tabbatar ba a sake mayar da Afghanistan wata matattarar ‘yan ta’adda ba.
Sa’o’i kadan gabanin sanarwar ta Shugaba Biden, kakakin Taliban Zabihullah Mujahid ya ce lallai Amurka ta kai wani hari da jirgi maras matuki a birnin Kabul, kuma ya yi tur da kai harin, sai dai bai ambaci sunan al Zawahiri ba.
Ya kuma ce harin ya saɓa wa tsarin kasa da kasa da ya hana wata ƙasa kai hari cikin wata kasar mai ‘yancin kai ba tare da amincewarta ba.
Sakataren harkokin waje na Amurka Anthony Blinken ya ce kungiyar Taliban ta saba wa yarjejeniyar da ta kulla da Amurka a birnin Doha, wanda a karkashinta Amurka ta janye dakarunta daga Afghanistan a bara.
A karkashin yarjejeniyar, Taliban ta amince ba za ta ƙyale ƙungiyoyin ‘yan ta’adda su yi amfani da kasar a matsayin wurin kitsa hare-hare kan kasashen yammacin duniya ba.