An yi taron tunawa da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya mai littattafan Tatsuniyoyi da Wasanni

321292965 509952567867389 8202321937612072262 n
321292965 509952567867389 8202321937612072262 n

Yayin da mashahurin marubucin littattafan hausa nan ya cika shekaru 27 da rasuwa, cibiyar binciken harsunan Najeriya da fassara da hikimomin al’umma ta Jami’ar Bayero Kano, ta gudanar da lakcar tuna wa da gagarumar gudummawar da ya bayar wajen bunkasa harshen Hausa.

Marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya ya rubuta litattafan Hausa masu yawa wadanda suka taimaka wajen bunkasa koyo da koyarwa a makarantu.

An gabatar da lakca, mai taken “Halaye da Dabi’u A Cikin Tatsuniyoyin Hausa” don tunawa da babban malami kuma jagora Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, wanda ya rasu shekaru 27 da suka gabata.

Farfesa Yakubu Azare wanda shi ne shugaban cibiyar binciken harsunan Najeriya jami’ar Bayero Kano da ya shirya lakcar.

Yace ”manufar wannan taron ita ce daga daraja da martaba da kimair marigayi, hakika ya ba da kyakkyawar gudummawa da hidimarsa ta fannin ilimi.

“Dalilin da ya sanya muka ga ya kamata duniya ta san abubuwan da ya yi, wanda har yanzu al’umma ke ci gaba da mora ta fanno ni da dama musamman bangaren bunkasa ilimi da harshen hausa,” in ji Farfesa Yakubu Azare.

Farfesa Lawan Dan Ladi Yalwa na tsangayar koyar da harsuna na daga cikin mahalarta taron, kuma ya gabatar da jawabi game da marifgayi Ibrahim Yaro Yahaya.

”An shirya taron lakcar, don ta zamo darasi ga ƴan baya su ji hikimomi da bajintar da babban malamin ya yi wajen bunkasa harshen Hausa, sannan su fadakar tare da koyon darusa.

“Hakika ya ba da gudummawa wajen bunkasa Adabi da Nahawu da sauransu.”

Marigayin ya rubuta littatafai har 16 ciki har da bayani kan adabi da al’ada da nahawu, sannan shi ne mutumin da ya fassara littafin dare sha biyu, wadanda suka zama jagora wajen kyautata harshen Hausa da bunkasa ilimi.

Ya kuma riki mahimman mukamai a Jami’ar Bayero Kano ciki har da mataimakin shugaban jami’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here