Mai shari’a S.C. Oriji na babban kotun babban birnin tarayya dake Maitama ya dage zaman shari’ar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Abubakar Sirika, zuwa ranar 9 ga watan Disamba, 2025 domin bangarorin masu gabatar da ƙara da masu kare kansu su gabatar da jawabansu a rubuce.
Ana gurfanar da Sirika tare da ‘yarsa, Fatima Hadi Sirika, da surukinsa Hamma Jalal Sule kan tuhuma guda shida da suka shafi amfani da muƙami ba bisa ka’ida ba da kuma halatta kuɗin haram, wanda adadinsa ya kai naira biliyan 2.7.
Musamman, ana zargin tsohon ministan da bai wa kamfanin Al Buraq Global Investment Limited, wanda ke da alaka da ‘yarsa, fifiko ba bisa doka ba a lokacin da yake kan mulki.
A zaman shari’ar da aka ci gaba da yi a ranar Talata, 28 ga Oktoba, 2025, alkalin kotun ya umurci lauyoyin biyu su gabatar da jawabansu na rubuce domin tantance bin ƙa’idojin sashe na 15 (4) da 17 (2) na dokar gudanar da shari’a ta laifuka (ACJA).
Wannan mataki ya biyo bayan korafin da masu kare wanda ake tuhuma na biyu da na uku da suka gabatar cewa ba a karɓi bayanansu a hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da yardarsu ba, lamarin da ya sa alkalin ya umarci a gudanar da shari’a cikin Shari’a domin tabbatar da gaskiyar lamarin.
A yayin shaidar da yake bayarwa, jami’in bincike kuma shaidar gwamnati na 12, Christopher Odofin, ya bayyana cewa wadanda ake tuhumar ba a kama su ba, an gayyace su ne zuwa hukumar tare da lauyoyinsu, kuma sun bayar da bayanansu cikin ‘yanci ba tare da tilastawa ba ko barazana.
Mai shari’a Oriji ya ƙara umartar cewa lauyoyin masu kare su, su gabatar da jawabansu a rubuce cikin kwanaki 14 daga ranar 29 ga Oktoba, sannan masu gabatar da ƙara su gabatar da nasu bayan karɓar na ɓangaren masu kare kansu.













































