Bashin N150bn: Ƴan kwangila sun fara tattaunawa da gwamnatin tarayya

Shugaban ƙungiyar ƴan Kwangila na Najeriya AICAN, Jackson Nwosu, ya bayyana cewa an fara tattaunawa tsakanin ƴan kwangilar da ke yin zanga-zanga da kuma gwamnatin tarayya kan bashin kuɗaɗen ayyuka da suke bi.

Nwosu ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Abuja bayan wata ganawa da jami’an ƙungiyar suka yi da Ministan Kuɗi, Wale Edun, inda ya ce an fara tattaunawa mai ma’ana domin warware matsalar.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan kwangila sun koma zanga-zanga tun ranar Talata, suna neman a biya su naira biliyan 150 daga cikin jimillar bashin naira tiriliyan 1.15 da suka ce gwamnati ke binsu.

A cewar su, bashin ya samo asali ne daga ayyukan gine-gine da suka aiwatar a sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da Babban Birnin Tarayya (FCT), a shekarar 2024.

Nwosu ya bayyana sakamakon ganawar a matsayin mai ƙarfafa gwiwa, yana mai cewa gwamnati ta bayar da shawarar biyan kashi 35 cikin ɗari na kuɗin nan take, sannan a biya ragowar a sannu a hankali cikin makonni masu zuwa.

Sai dai ya ce an umurci ‘yan kwangila su je su karɓi lambobin su (batch numbers) daga ma’aikatu da hukumomi daban-daban, yana mai nuna damuwa cewa lokacin da aka ba su ya yi kaɗan, tare da ƙarin bayani cewa waɗanda ba su da sabbin lambobi za su sake neman sabbin takardu domin biyan kuɗin nasu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here